1Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;
2Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;
3Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
4Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;
5Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,
6Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;
7Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai
8Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa;
9Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;
10Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.”
11Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
12bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.
13za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,