1Ya mutanena, ku ji koyarwata;
2Zan buɗe bakina da misalai,
3abin da muka ji muka kuma sani,
4Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;
5Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub
6don tsara na biye su san su,
7Ta haka za su dogara ga Allah
8Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba,
9Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna,
10ba su kiyaye alkawarin Allah ba
11Suka manta da abin da ya aikata,
12Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu
13Ya raba teku ya kuma bi da su ciki;
14Ya bishe su da girgije da rana
15Ya tsage duwatsu a cikin hamada
16ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga
17Amma suka ci gaba da yin masa zunubi,
18Da gangan suka gwada Allah
19Suka yi magana a kan Allah,
20Sa’ad da ya bugi dutse,
21Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai;
22gama ba su gaskata ga Allah ba
23Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa
24ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci,
25Mutane suka ci burodin mala’iku;
26Ya saki iskar gabas daga sammai
27Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura,
28Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu,
29Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su,
30Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi,
31fushin Allah ya ƙuna a kansu;
32Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi;
33Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza
34A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi;
35Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu,
36Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki,
37zukatansu ba sa biyayya gare shi,
38Duk da haka ya kasance mai jinƙai;
39Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai,
40Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada
41Sau da sau suka riƙa gwada Allah;
42Ba su tuna da ikonsa,
43ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar
44Ya mai da kogunansu suka zama jini;
45Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su,
46Ya ba da hatsinsu ga fāra,
47Ya lalace inabinsu da ƙanƙara
48Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara,
49Ya saki musu fushinsa mai zafi,
50Ya shirya hanya wa fushinsa;
51Ya bugi kowane ɗan fari na Masar,
52Amma ya fitar da mutanensa kamar garke;
53Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro;
54Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki,
55Ya kori al’ummai a gabansu
56Amma suka gwada Allah
57Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci,
58Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu;
59Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai;
60Ya yashe tabanakul na Shilo,
61Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta,
62Ya ba da mutanensa ga takobi;
63Wuta ta cinye matasansu maza,
64aka karkashe firistocinsu,
65Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa,
66Ya kori abokan gābansa;
67Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf,
68amma ya zaɓi kabilar Yahuda,
69Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa,
70Ya zaɓi Dawuda bawansa
71daga kiwon tumaki ya kawo shi
72Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya;