1Ka ji kukata, ya Allah;
2Daga iyakar duniya na yi kira gare ka,
3Gama kai ne mafakata,
4Ina marmari in zauna a tentinka har abada
5Gama ka ji alkawarina, ya Allah;
6Ka ƙara kwanakin ran sarki,
7Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada;
8Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka