1Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.
2Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;
3Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
4Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni;
5Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni;
6Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;
7Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza,
8Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa;
9Ya buɗe sammai ya sauko;
10Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya;
11Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi,
12daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba,
13Ubangiji ya yi tsawa daga sama;
14Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba,
15Kwarin teku sun bayyana
16Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni;
17Ya cece ni daga abokin gābana mai ƙarfi,
18Sun yi arangama da ni a ranar masifa,
19Ya fitar da ni zuwa wuri mai sarari;
20Ubangiji ya yi haka da ni bisa ga adalcina;
21Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji;
22Dukan dokokinsa suna a gābana;
23Na kasance marar laifi a gabansa
24Ubangiji ya ba ni lada bisa ga adalcina,
25Ga mai aminci ka nuna kanka mai aminci,
26ga mai tsabta ka nuna kanka mai tsabta,
27Kakan cece mai sauƙinkai
28Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci;
29Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna;
30Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce;
31Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba?
32Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi
33Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa;
34Ya horar da hannuwana don yaƙi;
35Ka ba ni garkuwar nasara,
36Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina,
37Na bi abokan gābana na kuma cim musu;
38Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba;
39Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi;
40Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu,
41Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba,
42Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa;
43Ka cece ni daga harin mutane;
44da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya;
45Duk sukan karai;
46Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena!
47Shi ne Allah mai sāka mini,
48wanda yakan cece ni daga abokan gābana.
49Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji;
50Yakan ba sarkinsa nasarori;