1Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye;
2masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu
3Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji;
4Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye;
5Masu girman kai sun sa mini tarko;
6Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.”
7Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi,
8Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji;
9Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni
10Bari garwashin wuta yă zubo a kansu;
11Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar;
12Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci
13Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka