1Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi.
2Ku yi godiya ga Allahn alloli.
3Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji.
4Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki,
5Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai,
6Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye,
7Wanda ya yi manyan haskoki,
8Rana don tă yi mulkin yini,
9Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare;
10Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar
11Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu
12Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko;
13Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu
14Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa,
15Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku;
16Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada,
17Wanda ya buge manyan sarakuna,
18Ya karkashe manyan sarakuna,
19Sihon sarkin Amoriyawa
20Da kuma Og sarkin Bashan,
21Ya kuma ba da ƙasarsu gādo,
22Gādo ga bawansa Isra’ila;
23Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu
24Ya kuma ’yantar da mu daga abokan gābanmu,
25Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta.
26Ku yi godiya ga Allah na sama.