1Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi,
2in maganarka ta taɓa kama ka,
3to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka;
4Ka hana kanka barci,
5Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta,
6Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;
7Ba shi da jagora
8duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani
9Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?
10Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,
11talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari
12Sakare da mutumin banza
13wanda yake ƙyifce da ido,
14wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa,
15Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya;
16Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,
17duban reni,
18zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,
19mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,
20Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka
21Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;
22Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;
23Gama waɗannan umarnai fitila ne,
24suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a
25Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka
26Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta,
27Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa
28Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi
29Haka yake da wanda ya kwana da matar wani;
30Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata
31Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai
32Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;
33Dūka da kunya ne za su zama rabonsa,
34Gama kishi kan tā da hasalar miji,
35Ba zai karɓi duk wata biya ba;