1Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne;
2Fushin sarki yana kama da rurin zaki;
3Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa,
4Rago ba ya noma a lokacin noma;
5Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne,
6Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne,
7Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;
8Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a,
9Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki;
10Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba,
11Akan san ƙananan yara ta ayyukansu,
12Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani,
13Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;
14“Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya;
15Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace,
16A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo;
17Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi,
18Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara;
19Mai gulma yakan lalace yarda;
20In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa,
21Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa
22Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!”
23Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba,
24Ubangiji ne yake bi da matakan mutum,
25Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani
26Sarki mai hikima yakan gane mugunta;
27Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum
28Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya;
29Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu,
30Naushi da rauni kan share mugunta,