1Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke,
2Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi,
3Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi,
4Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa,
5Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai.
6Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi;
7Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji,
8Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci
9’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu,
10Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah,
11Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne;
12Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau,
13Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya;
14Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne,
15Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan;
16Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya,
17Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta;
18Girmankai yakan zo kafin hallaka,
19Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai,
20Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara,
21Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai,
22Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi,
23Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa,
24Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,
25Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum,
26Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki;
27Mutumin banza yakan ƙulla mugunta,
28Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali,
29Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa
30Duk wanda ya ƙyifce da idonsa yana ƙulla maƙarƙashiya ce;
31Furfura rawani ne mai daraja;
32Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi,
33Akan jefa ƙuri’a a kan cinya,