1Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani,
2Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji,
3Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta,
4Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne,
5Shirye-shiryen masu adalci daidai ne,
6Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai,
7Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu,
8Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa,
9Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa
10Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa,
11Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace,
12Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane,
13Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi,
14Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau
15Hanyar wawa daidai take a gare shi,
16Wawa kan nuna fushinsa nan take,
17Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya,
18Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi,
19Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,
20Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta,
21Ba wani lahanin da zai sami masu adalci,
22Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,
23Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa,
24Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki,
25Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,
26Adali yakan yi hankali a abokantaka,
27Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta,
28A hanyar adalci akwai rai;