1“Ku yi ta kai da kawowa a titunan Urushalima,
2Ko da yake suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’
3Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya?
4Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta;
5Saboda haka zan tafi wurin shugabanni
6Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu,
7“Me zai sa in gafarta muku?
8An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu,
9Ba zan hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji.
10“Ku ratsa cikin gonakin inabinta ku cinye su,
11Gidan Isra’ila da gidan Yahuda
12Sun yi ƙarya a kan Ubangiji;
13Annabawa holoƙo ne kawai
14Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa,
15Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji,
16Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne;
17Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku,
18“Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba.
19Sa’ad da kuma mutanen suka yi tambaya, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi dukan wannan gare mu?’ Sai ka amsa musu, ‘Yadda kuka yashe ni kuka kuma bauta wa baƙin alloli a ƙasarku, haka yanzu za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’
20“Ka sanar da wannan ga gidan Yaƙub
21Ku ji wannan, ku wawaye marasa azanci,
22Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji.
23Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne;
24Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu,
25Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa;
26“A cikin mutanena an sami mugaye
27Kamar keji cike da tsuntsaye,
28suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul.
29Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?”
30“Abin banmamaki da bantsoro
31Annabawa suna annabcin ƙarya,