1“In mutum ya saki matarsa
2“Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani.
3Saboda haka an hana yayyafi,
4Yanzu ba kin kira ni,
5kullum za ka riƙa fushi?
6A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can.
7Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani.
8Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina.
9Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace.
10Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji.
11Ubangiji ya ce mini, “Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci.
12Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa,
13Ki dai yarda da laifinki
14“Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona.
15Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi.
16A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.
17A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba.
18A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.
19“Ni kaina na faɗa,
20Amma kamar mace marar aminci ga mijinta,
21An ji kuka a filayen tuddai,
22“Ku komo, mutane marasa bangaskiya;
23Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai
24Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu
25Bari mu kwanta mu sha kunya,