1Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Tafi ka sayo abin ɗamara na lilin ka sha ɗamara da shi, amma kada ka bari yă taɓa ruwa.”
2Saboda haka na sayo abin ɗamara, yadda Ubangiji ya umarce ni, na kuwa sha ɗamara da shi.
3Sai maganar Ubangiji ta zo mini sau na biyu cewa,
4“Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi yanzu zuwa Fera13.4 Ko kuwa mai yiwuwa Yuferites; haka ma a ayoyi 5-7 ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.”
5Saboda haka na tafi na ɓoye shi a Fera, yadda Ubangiji ya ce mini.
6Bayan ’yan kwanaki sai Ubangiji ya ce mini, “Tafi yanzu zuwa Fera ka ɗauko abin ɗamara da na ce maka ka ɓoye a can.”
7Sai na tafi Fera da haka na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi, amma abin ɗamara yanzu ya lalace ya zama ba shi da amfani sam.
8Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
9“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Haka zan lalatar da alfarmar Yahuda da yawan alfarmar Urushalima.
10Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani!
11Gama kamar yadda abin ɗamara kan kame gindin mutum tam, haka zan daure dukan gidan Isra’ila da dukan gidan Yahuda gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘domin su zama jama’a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.’
12“Faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi.’ In kuwa suka ce maka, ‘Ba mu san cewa ya kamata a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi ba?’
13Sai ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan cika dukan waɗanda suke zama a ƙasar da buguwa, har ma da sarakunan da suke zama a kursiyin Dawuda, firistoci, annabawa da dukan waɗanda suke zaune a Urushalima.
14Zan fyaɗe su a kan juna, iyaye da ’ya’yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi ko jinƙai, ko juyayi ba zai hana ni hallaka su ba.’ ”
15Ku ji ku kuma saurara,
16Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku
17Amma in ba ku saurara ba,
18Ka faɗa wa sarki da kuma mahaifiyar sarauniya cewa,
19Za a kulle biranen da suke a Negeb,
20Ku tā da idanunku ku ga
21Me za ku ce sa’ad da Ubangiji ya naɗa muku
22In kuma kuka tambaye kanku
23Mutumin Habasha13.23 Da Ibraniyanci Mutumin Kush (mai yiwuwa mutum daga yankin Bisa na Nilu). zai iya canja launin fatar jikinsa
24“Zan watsar da ku kamar yayin
25Rabonku ne wannan,
26Zan kware fatarinku sama ya rufe fuskarku
27zinace zinacenku da haniniya kamar dawakai,