1Sai Ayuba ya amsa,
2“Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan;
3Dogayen surutanku ba sa ƙare ne?
4Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi
5Amma bakina zai ƙarfafa ku;
6“Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi;
7Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni;
8Ka daure ni, ya kuma zama shaida;
9Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa
10Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni;
11Allah ya bashe ni ga mugayen mutane,
12Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai;
13maharbansa sun kewaye ni.
14Ya ji mini rauni a kai a kai
15“Ina makoki saye da tsummoki
16Fuskata ta yi ja don kuka
17duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba
18“Ya duniya, kada ki ɓoye jinina;
19Ko yanzu haka shaidata tana sama;
20Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne
21a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah
22“Shekaru kaɗan suka rage