We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Ishaya 30

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Ishaya 29 Ishaya Ishaya 31 →

1“Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,”

2waɗanda suka gangara zuwa Masar

3Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya,

4Ko da yake suna da shugabanni a Zowan

5kowa zai sha kunya

6Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa,

7zuwa Masar, wadda taimakonta marar amfani ne.

8Tafi yanzu, ka rubuta musu a kan allo,

9Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu,

10Sukan ce wa masu gani,

11Ku bar wannan hanya,

12Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa,

13wannan zunubi zai zama muku

14Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu,

15Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa,

16Kun ce, ‘A’a, za mu gudu a kan dawakai.’

17Dubu za su gudu

18Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;

19Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku.

20Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su.

21Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.”

22Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!”

23Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya.

24Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali.

25A ranar babban kisa, sa’ad da hasumiyoyi za su fāɗi, rafuffukan ruwa za su malalo a kan kowane dutse da kowane tudu mai tsawo.

26Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.

27Duba, Sunan Ubangiji yana zuwa daga nesa,

28Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu

29Za ku kuma rera

30Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja

31Muryar Ubangiji za tă firgita Assuriya

32Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu

33An riga an shirya wurin ƙonawa;

← Ishaya 29 Ishaya Ishaya 31 →