We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Mai Hadishi 6

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Mai Hadishi 5 Mai Hadishi Mai Hadishi 7 →

1Na ga wani mugun abu a duniya, ya kuma nawaita wa mutane ƙwarai.

2Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai.

3Mutum zai iya kasance da ’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa.

4Haihuwa ba tă amfane wanda aka haifa gawa ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi.

5Ko da yake bai ga hasken rana ba, bai kuma san kome ba, duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa ransa ba,

6ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba?

7Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa,

8Da me mai hikima ya fi wawa?

9Gara abin da ido ya gani

10Duk abin da ya kasance, to, yana da suna,

11Yadda yawan magana take

12Gama wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a ’yan kwanakinsa marasa amfani da sukan wuce kamar inuwa? Wa kuma zai iya faɗa masa abin da zai faru a duniya bayan ya rasu?

← Mai Hadishi 5 Mai Hadishi Mai Hadishi 7 →