1Ka lura da matakanka sa’ad da ka tafi gidan Allah. Ka je kusa don ka saurara a maimakon miƙa hadaya kamar wawaye, waɗanda ba su san sun yi laifi ba.
2Kada ka yi subul da bakinka,
3Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa,
4Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka.
5Gara kada ka yi alkawari, da ka yi amma ba ka cika ba.
6Kada ka bar bakinka ya kai ga yin zunubi. Kada kuma ka kai ƙara wurin ɗan saƙon haikali cewa, “Alkawarin da na yi kuskure ne.” Me ya sa Allah yake fushi a kan abin da ka faɗa har yă lalatar da aikin hannuwanka?
7Yawan buri da yawan magana ba su da amfani. Saboda haka, ka ji tsoron Allah.
8In ka ga ana zaluntar matalauta a wani yanki, ba a yin adalci, ana kuma tauye hakki, kada ka yi mamakin waɗannan abubuwa; domin akwai wani jami’in da yake bisa da wani, a bisansu biyu kuwa akwai wani.
9Kowa yakan amfana da bunkasar amfanin ƙasa, sarki kansa yana samun riba daga gonaki.
10Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe;
11Kamar yadda kaya suke haɓaka,
12Barcin ma’aikaci daɗi gare shi,
13Na ga wani mugun abu a duniya,
14ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara,
15Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa,
16Wannan ma mugun abu ne,
17Duk rayuwarsa ya ci abinci a cikin duhu,
18Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa.
19Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah.
20Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki.