1Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne,
2Meshelemiya yana da ’ya’ya maza.
3Elam na biyar, Yehohanan na shida
4Obed-Edom shi ma yana da ’ya’ya maza.
5Ammiyel na shida,
6Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da ’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai.
7’Ya’yan Shemahiya maza su ne,
8Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.
9Meshelemiya yana da ’ya’ya maza da kuma ’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka.
10Hosa dangin Merari yana da ’ya’ya maza.
11Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku
12Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi.
13Aka jefa ƙuri’u don kowace ƙofa bisa ga iyalansu, ƙarami da babba.
14Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya.
15Ƙuri’a don Ƙofar Kudu ta fāɗo a kan Obed-Edom, ƙuri’a don ɗakin ajiya kuwa ta fāɗo a kan ’ya’yansa maza.
16Ƙuri’u don Ƙofar Yamma da kuma Ƙofar Shalleket a hanyar bisa suka fāɗo a kan Shuffim da Hosa.
17Akwai Lawiyawa shida da suke tsaron ƙofar gabas,
18Game da filin waje ta yamma kuwa, akwai masu tsaro huɗu a hanya da kuma biyu a filin26.18 Ma’anar wannan a Ibraniyanci babu tabbas. kansa.
19Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari.
20’Yan’uwansu Lawiyawa kuwa su ne26.20 Seftuwajin; Ibraniyanci Game da Lawiyawa kuwa, Ahiya ne suke lura da ma’ajin gidan Allah da kuma baitulmali don kayayyakin da aka keɓe.
21Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli,
22’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel. Su ne suke kula da ma’ajin haikalin Ubangiji.
23Daga zuriyar Amram, Izhar, mutanen Hebron da kuma Uzziyel, su ma aka ba su aiki.
24Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’i mai lura da baitulmali.
25Danginsa na wajen Eliyezer su ne, Rehabiya, Yeshahiya, Yoram, Zikri da Shelomit.
26Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa.
27Sun keɓe waɗansu ganimar da aka kwaso a yaƙi don gyaran haikalin Ubangiji.
28Shelomit da ’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe.
29Daga mutanen Izhar,
30Daga zuriyar Hebron,
31Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu.
32Yeriya yana da ’yan’uwa guda dubu biyu da ɗari bakwai, jarumawa da kuma kawunan iyalai, sai Sarki Dawuda ya sa su lura da mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse game da kome da ya shafi Allah da kuma al’amuran sarki.