We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

1 Tarihi 27

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← 1 Tarihi 26 1 Tarihi 1 Tarihi 28 →

1Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000.

2Wanda yake lura da sashe na fari, na wata na farko, shi ne Yashobeyam ɗan Zabdiyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

3Shi zuriyar Ferez ne kuma babba na dukan shugabannin mayaƙa don wata na farko.

4Wanda yake lura da sashen don wata na biyu shi ne Dodai mutumin Ahowa; Miklot ne shugaban sashensa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

5Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. Shi ne babba kuma akwai mutane 24,000 a sashensa.

6Wannan shi ne Benahiya wanda yake ɗaya daga cikin jarumawa Talatin nan kuma shi ne yake babba a cikin Talatin ɗin. Ɗansa Ammizabad ne yake lura da sashensa.

7Na huɗu, don wata na huɗu, shi ne Asahel ɗan’uwan Yowab; ɗansa Zebadiya shi ne magājinsa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

8Na biyar don wata na biyar, shi ne Shamhut mutumin Izhar shugaban mayaƙa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

9Na shida, don wata na shida, shi ne Ira ɗan Ikkesh mutumin Tekowa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

10Na Bakwai, don wata na bakwai, shi ne Helez mutumin Felon, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

11Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

12Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

13Na goma, don wata na goma, shi ne Maharai mutumin Netofa, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

14Na goma sha ɗaya, don wata goma sha ɗaya, shi ne Benahiya mutumin Firaton, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

15Na goma sha biyu don wata goma sha biyu, shi ne Heldai mutumin Netofa, daga iyalin Otniyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

16Shugabannin da suke bisa kabilan Isra’ila,

17bisa mutanen Lawi shi ne, Hashabiya ɗan Kemuwel;

18bisa mutanen Yahuda shi ne, Elihu, ɗan’uwan Dawuda;

19bisa mutanen Zebulun shi ne, Ishmahiya ɗan Obadiya;

20bisa mutanen Efraim shi ne, Hosheya ɗan Azaziya;

21bisa ɗayan rabi kabilar Manasse a Gileyad shi ne, Iddo ɗan Zakariya;

22bisa mutanen Dan shi ne, Azarel ɗan Yeroham.

23Dawuda bai ƙirga mutanen da suke ’yan shekara ashirin ko ƙasa ba, domin Ubangiji ya yi alkawari zai sa Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.

24Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba.

25Azmawet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ɗakuna ajiyar fada.

26Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da ma’aikatan gona waɗanda suke nome ƙasar.

27Shimeyi mutumin Ramat shi ne mai lura da gonakin inabi.

28Ba’al-Hanan mutumin Geder shi ne mai lura da itatuwan zaitun da na al’ul a gindin tuddan yamma.

29Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon.

30Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma.

31Yaziz mutumin Hagiri shi ne mai lura da tumaki.

32Yonatan, kawun Dawuda, shi ne mashawarci, mutum mai hangen nesa kuma marubuci.

33Ahitofel shi ne mashawarcin sarki.

34Yehohiyada ɗan Benahiya da Abiyatar ne suka gāji Ahitofel.

← 1 Tarihi 26 1 Tarihi 1 Tarihi 28 →