1Sai mala’ikan da ya yi magana da ni ya komo ya farkar da ni, kamar yadda ake farkar da mutum daga barcinsa.
2Ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”
3Akwai kuma itatuwan zaitun guda biyu a gefensa, ɗaya a gefen dama na kwanon ɗaya kuma a gefen hagunsa.”
4Na tambayi mala’ikan da ya yi magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?”
5Sai ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?”
6Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
7“Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ”
8Sai maganar Ubangiji ta zo mini,
9“Hannuwan Zerubbabel sun kafa harsashin haikalin nan; hannuwansa ne kuma za su gama ginin. Sa’an nan ne za ka san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni zuwa wurinka.
10“Wa ya rena ranar ƙananan abubuwa? Mutane za su yi murna sa’ad da suka ga igiyar gwaji a hannun Zerubbabel.
11Sai na tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan itatuwan zaitun guda biyu tsaye a hagu da kuma daman wurin ajiye fitilan fitilu?”
12Na sāke tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan rassa biyun nan na zaitun a gefen bututu biyu na zinariya da suke zuba man zinariya?”
13Ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?”
14Sai ya ce, “Waɗannan su ne biyun da aka shafe don4.14 ko kuwa biyun da suke kawo mai su kuma su yi wa Ubangiji dukan duniya hidima.”