1Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara.
2Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun;
3Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi,
4Ka tace azurfa
5ka cire mugaye daga gaban sarki,
6Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki,
7gara ya ce maka, “Ka hauro nan,”
8kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa,
9In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama,
10in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka
11Kalmar da aka faɗa daidai
12Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla
13Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi
14Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama
15Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki,
16In ka sami zuma, ka sha isashe kawai,
17Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka
18Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini
19Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa
20Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi,
21In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci;
22Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa,
23Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama,
24Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki
25Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji
26Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace
27Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa,
28Kamar birni da katangarsa sun rushe