1Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki,
2ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka
3Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi
4Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki;
5Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace,
6Kada ka ci abincin mai rowa,
7gama shi wani irin mutum ne
8Za ka yi amai ɗan abin da ka ci
9Kada ka yi magana da wawa,
10Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā
11gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi;
12Ka mai da hankali ga umarni
13Kada ka bar yaro ba horo;
14Ka hukunta shi da sanda
15Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce,
16cikin cikina zai yi farin ciki
17Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi,
18Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka,
19Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima,
20Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa
21gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta,
22Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,
23Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;
24Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;
25Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna;
26Ɗana, ka ba ni zuciyarka
27gama karuwa rami ne mai zurfi
28Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira
29Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki?
30Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi,
31Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja,
32A ƙarshe yana sara kamar maciji
33Idanunka za su riƙa gane-gane,
34Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna,
35Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba!