1Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.
2Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;
3don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,
4don sa marar azanci yă yi hankali,
5bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,
6don su fahimci karin magana da kuma misalai,
7Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
8Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
9Za su zama kayan ado don su inganta ka
10Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka,
11In suka ce, “Zo mu tafi;
12mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari,
13za mu sami dukiya masu daraja iri-iri,
14ka haɗa kai da mu,
15ɗana, kada ka tafi tare da su,
16gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi,
17Ba shi da amfani a kafa tarko
18Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko;
19Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau;
20Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi,
21tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu,1.21 Da Ibraniyanci; Seftuwajin / a bisa katanga
22“Har yaushe ku da kuke marasa azanci1.22 Kalmar Ibraniyancin da aka rubuta marar azanci a cikin Littafin Kari Magana gaba ɗaya tana nufin marar ɗa’a da kuma wanda yana aikata mugunta ne. za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci?
23Da a ce kun saurari tsawatata,
24Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira
25da yake kun ƙi dukan shawarata
26Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku,
27sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri,
28“Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba;
29Da yake sun ƙi sani
30da yake ba su karɓi shawarata ba
31za su sami sakayyar abubuwan da suka yi
32Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su,
33amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya