1Ubangiji ya ce wa Musa,
2“Ka umarci Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga Kan’ana, ƙasar da aka ba ku gādo za tă kasance da waɗannan iyakoki.
3“ ‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,34.3 Wato, Mataccen Teku; haka ma a aya 12.
4tă ƙetare Mashigin Kunama34.4 Da Ibraniyanci Akrabbim a kudu, tă ci gaba zuwa Zin, sa’an nan tă nufi kudu da Kadesh Barneya. Sa’an nan za tă zarce zuwa Hazar Addar, tă nausa zuwa Azmon,
5inda za tă juya tă haɗu da Rafin Masar, tă kuma ƙarasa a Bahar Rum.34.5 Wato, Mediterraniyan; haka kuma a ayoyi 6 da 7.
6“ ‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.
7“ ‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor,
8za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo34.8 Ko Kuwa zuwa mashigin Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad,
9tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa.
10“ ‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam.
11Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret.34.11 Wato, Galili
12Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri.
13Sai Musa ya umarci Isra’ilawa ya ce, “Ku raba wannan ƙasa da za ku gāda ta hanyar jefa ƙuri’a. Ubangiji ya umarta cewa a ba da ita ga kabilu tara da rabi,
14saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu.
15Waɗannan kabilu biyu da rabi, sun sami gādonsu a wancan hayin Urdun a gabashin Yeriko34.15 Urdun na Yeriko mai yiwuwa tsohuwar suna ce ta Kogin Urdun. wajen fitowar rana.”
16Ubangiji ya ce wa Musa,
17“Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.
18Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.
19“Ga sunayensu.
20Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon
21Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;
22Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;
23Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;
24Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;
25Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;
26Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;
27Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;
28Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”
29Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.