1Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar.
2Bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tafiye-tafiyensu da sansaninsu. Ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance.
3Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa,
4waɗanda suke binne gawawwakin ’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu.
5Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot.
6Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada.
7Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol.
8Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.
9Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can.
10Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.
11Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.
12Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka.
13Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush.
14Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.
15Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.
16Suka tashi daga Hamadan Sinai, suka yi sansani a Kibrot Hatta’awa.
17Suka tashi daga Kibrot Hatta’awa, suka yi sansani a Hazerot.
18Suka tashi daga Hazerot, suka yi sansani a Ritma.
19Suka tashi daga Ritma, suka yi sansani a Rimmon Ferez.
20Suka tashi daga Rimmon Ferez, suka yi sansani a Libna.
21Suka tashi daga Libna, suka yi sansani a Rissa.
22Suka tashi daga Rissa, suka yi sansani a Kehelata.
23Suka tashi daga Kehelata, suka yi sansani a Dutsen Shefer.
24Suka tashi daga Dutsen Shefer, suka yi sansani a Harada.
25Suka tashi daga Harada, suka yi sansani a Makhelot.
26Suka tashi daga Makhelot, suka yi sansani a Tahat.
27Suka tashi daga Tahat, suka yi sansani a Tera.
28Suka tashi daga Tera, suka yi sansani a Mitka.
29Suka tashi daga Mitka, suka yi sansani a Hashmona.
30Suka tashi daga Hashmona, suka yi sansani a Moserot.
31Suka tashi daga Moserot, suka yi sansani a Bene Ya’akan.
32Suka tashi daga Bene Ya’akan, suka yi sansani a Hor Haggidgad.
33Suka tashi daga Hor Haggidgad, suka yi sansani a Yotbata.
34Suka tashi daga Yotbata, suka yi sansani a Abrona.
35Suka tashi daga Abrona, suka yi sansani a Eziyon Geber.
36Suka tashi daga Eziyon Geber, suka yi sansani a Kadesh, cikin Hamadan Zin.
37Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom.
38Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar.
39Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor.
40Sarki Arad Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb na Kan’ana, ya ji labari cewa Isra’ilawa suna zuwa.
41Suka tashi daga Dutsen Hor, suka yi sansani a Zalmona.
42Suka tashi daga Zalmona, suka yi sansani a Funon.
43Suka tashi daga Funon, suka yi sansani a Obot.
44Suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim, a iyakar Mowab.
45Suka tashi daga Iyim33.45 Wato, Iye Abarim., suka yi sansani a Dibon Gad.
46Suka tashi daga Dibon Gad, suka yi sansani a Almon Dibilatayim.
47Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo.
48Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.
49A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim.
50A filayen Mowab kusa da Urdun ɗaura da Yeriko ne Ubangiji ya ce wa Musa,
51“Ka gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana,
52ku kori dukan mazaunan ƙasar a gabanku. Ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsu, da siffofinsu na zubi, ku kuma rurrushe dukan masujadansu na kan tudu.
53Ku mallaki ƙasar, ku kuma zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta.
54Ku rarraba ƙasar ta wurin jefan ƙuri’a, bisa ga kabilanku. Kabilar da take babba, a ba ta babban gādo, ƙarami kabila kuwa, a ba ta ƙaramin gādo. Duk abin da ƙuri’a ta ba su, shi zai zama nasu. Ku rarraba wannan bisa zuriyar kakanninku.
55“ ‘Amma in ba ku kori mazaunan ƙasar ba, waɗanda kuka bari su ci gaba da zama, za su zama muku hakki a idanunku, da kuma ƙayayyuwa a bayanku. Za su ba ku wahala a ƙasar da kuke zama.
56Sa’an nan kuwa zan yi muku abin da na shirya yin musu.’ ”