1Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
2“Duk surutun nan ba za a amsa maka ba?
3Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru?
4Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne
5Da ma Allah zai yi magana,
6yă kuma buɗe maka asirin hikima,
7“Ko za ka iya gane al’amuran Allah?
8Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi?
9Tsayinsu ya fi tsawon duniya
10“In ya zo ya kulle ka a kurkuku
11Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya;
12Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima
13“Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka,
14in ka kawar da zunubin da yake hannunka,
15shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba;
16Ba shakka za ka manta da wahalolinka,
17Rayuwarka za tă fi hasken rana haske,
18Za ka zauna lafiya, domin akwai bege;
19Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro,
20Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba,