We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Irmiya 45

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Irmiya 44 Irmiya Irmiya 46 →

1Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa,

2“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk.

3Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’ ”

4Ubangiji ya ce, “Ka faɗa masa wannan, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan rushe abin da na gina in kuma tumɓuke abin da na dasa, a duk fāɗin ƙasar.

5Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’ ”

← Irmiya 44 Irmiya Irmiya 46 →