We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Ayuba 42

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Ayuba 41 Ayuba

1Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji,

2“Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa;

3Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’

4“Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana

5Kunnuwana sun ji game da kai

6Saboda haka na rena kaina

7Bayan Ubangiji ya gaya wa Ayuba waɗannan abubuwa, ya ce wa Elifaz mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokanka guda biyu domin ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.

8Saboda haka yanzu sai ku ɗauki bijimai guda bakwai, da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa hadaya ta ƙonawa domin kanku. Bawana Ayuba zai yi muku addu’a zan kuwa karɓi addu’arsa in bi da ku nisa da wawancinku. Ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba yadda bawana Ayuba ya yi ba.”

9Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba.

10Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu.

11Dukan ’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya.

12Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu.

13Ya kuma haifi ’ya’ya maza bakwai, mata uku.

14’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk.

15Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza.

16Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu.

17Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.

← Ayuba 41 Ayuba