1Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne.
2Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba.
3Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi.
4Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.
5Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata.
6Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce,
7Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana;
8Amma ruhun da yake cikin mutum,
9Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba,
10“Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni;
11Na jira sa’ad da kuke magana,
12na saurare ku da kyau.
13Kada ku ce, ‘Mun sami hikima;
14Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba
15“Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa;
16Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru,
17Ni ma zan faɗi nawa;
18Gama ina cike da magana,
19a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba,
20Dole in yi magana in sami lafiya;
21Ba zan nuna wa wani sonkai ba,
22gama da a ce na iya daɗin baki,