1“Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce;
2Zan yi magana;
3Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata;
4Ruhun Allah ne ya yi ni;
5Ka amsa mini in za ka iya;
6Ni kamar ka nake a gaban Allah;
7Kada ka ji tsorona,
8“Amma ka faɗa na ji,
9‘ni mai tsarki ne marar zunubi;
10Duk da haka Allah ya same ni da laifi;
11ya daure ƙafafuna da sarƙa;
12“Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba,
13Don me ka yi masa gunaguni
14Gama Allah yana magana,
15A cikin mafarki, cikin wahayi da dare,
16mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu
17don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba
18don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami,
19“Ko kuma mutum yă sha horo
20yadda zai ji ƙyamar abinci,
21Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki
22Ransa yana matsawa kusa da rami,
23Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci,
24yă yi masa alheri yă ce,
25Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri;
26Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa,
27Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce,
28Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami,
29“Allah ya yi wa mutum duk waɗannan,
30Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami,
31“Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni;
32In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini;
33Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni;