1Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
2“Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gado
3Ko zai yi gardama da maganganun wofi
4Amma ka ma rena Allah
5Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce;
6Bakinka zai kai ka yă baro, ba nawa ba;
7“Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa?
8Kana sauraron shawarar Allah?
9Me ka sani da ba mu sani ba?
10Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu
11Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba.
12Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka,
13har kake fushi da Allah
14“Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki,
15In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba,
16mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa,
17“Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani;
18abin da masu hikima suka ce,
19(waɗanda su ne masu ƙasar
20Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala,
21Ƙara mai bantsoro za tă cika kunnuwansa
22Yana jin tsoron duhu
23Yana ta yawo, abinci don ungulaye;15.23 Ko kuwa yawo, neman abinci
24Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi,
25domin ya nuna wa Allah yatsa
26ya tasar masa da faɗa
27“Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu
28zai yi gādon garuruwan da suka lalace,
29Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba,
30Ba zai tsere wa duhu ba;
31Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani
32Kafin lokacinsa yă cika, za a gama biyansa duka,
33Zai zama kamar itacen inabi wanda ’ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna,
34Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da ’ya’ya,
35Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta;