We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Ishaya 8

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Ishaya 7 Ishaya Ishaya 9 →

1Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz.8.1 Maher-Shalal-Hash-Baz yana nufin kwashe ganima nan da nan, washe kayan da aka ci a yaƙi da hanzari; haka ma a 3.

2Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.”

3Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz.

4Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”

5Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,

6“Domin wannan jama’a ta ƙi

7saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu

8Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta,

9Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro!

10Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba;

11Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce,

12“Kada ka kira wani abu makirci

13Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki,

14zai kuwa kasance a wuri mai tsarki;

15Yawancinsu za su yi tuntuɓe;

16Ɗaura shaidar nan ta gargadi

17Zan saurari Ubangiji,

18Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona.

19Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai?

20Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani.

21Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu.

22Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.

← Ishaya 7 Ishaya Ishaya 9 →