We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Ishaya 19

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Ishaya 18 Ishaya Ishaya 20 →

1Abin da Allah ya faɗa game da Masar,

2“Zan tā da hargitsi tsakanin mutumin Masar da mutumin Masar,

3Masarawa za su karai,

4Zan ba da Masarawa

5Ruwayen kogi za su ƙafe,

6Wuriyoyi za su yi wari;

7haka ma tsire-tsire kusa da Nilu,

8Masu kamun kifi za su yi nishi su kuma yi makoki,

9Waɗanda suke aiki da kaɗin auduga za su karai,

10Masu aikin tufafi ransu zai ɓace,

11Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai;

12Ina masu hikima suke yanzu?

13Shugabannin Zowan sun zama wawaye,

14Ubangiji ya sa zuba musu

15Babu abin da Masar za tă yi,

16A wannan rana Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki lokacin da Ubangiji Maɗaukaki ya ɗaga hannu a kansu.

17Ƙasar Yahuda kuma za kawo fargaba ga Masarawa; kowanne da Yahuda ya ambace zai firgita, saboda abin da Ubangiji Maɗaukaki yake shiri a kansu.

18A wannan rana birane biyar a Masar za su yi yaren Kan’ana su kuma miƙa kai cikin yarjejjeniya ga Ubangiji Maɗaukaki. Za a ce da ɗayansu Birnin Hallaka.

19A wannan rana za a kasance da bagade ga Ubangiji a tsakiyar Masar, da kuma ginshiƙin dutse Ubangiji a iyakarta.

20Zai zama alama da kuma shaida ga Ubangiji Maɗaukaki a ƙasar Masar. Sa’ad da suka yi kuka ga Ubangiji saboda masu zaluntarsu, zai aiko musu mai ceto da mai kāriya, zai kuma cece su.

21Saboda haka Ubangiji zai sanar da kansa ga Masarawa, kuma a wannan rana za su yarda da Ubangiji. Za su yi masa sujada da hadayu da hadayun hatsi; za su yi alkawura ga Ubangiji su kuma kiyaye su.

22Ubangiji zai bugi Masar da annoba; zai buge su ya kuma warkar da su. Za su juyo wurin Ubangiji, zai amsa roƙonsu ya kuma warkar da su.

23A wannan rana za a kasance da babban hanya daga Masar zuwa Assuriya. Assuriyawa za su tafi Masar, Masarawa kuma za su tafi Assuriya. Masarawa da Assuriyawa za su yi sujada tare.

24A wannan rana Isra’ila za tă zama na uku, tare da Masar da Assuriya, abin albarka ga duniya.

25Ubangiji Maɗaukaki zai albarkace su, yana cewa, “Albarka ta tabbata ga Masar, mutanena, Assuriya aikin hannuna, da kuma Isra’ila gādona.”

← Ishaya 18 Ishaya Ishaya 20 →