1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2“Ɗan mutum, ka faɗa wa mai mulkin Taya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
3Ka fi Daniyel hikima ne?28.3 Ko kuwa Danel; yadda aka rubuta Ibraniyanci na wannan suna zai yi kamar ana zance wani dabam ne da annabi Daniyel.
4Ta wurin hikimarka da ganewarka
5Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci
6“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
7zan kawo baƙi a kanka,
8Za su jefar da kai cikin rami,
9Za ka iya ce yanzu, “Ni allah ne,”
10Za ka yi mutuwar marar kaciya
11Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
12“Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
13Ka kasance a Eden,
14An shafe ka kamar kerub mai tsaro,
15Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka
16Ta wurin yawan kasuwancinka
17Zuciyarka ta cika da alfarma
18Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta
19Dukan al’umman da suka san ka
20Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
21“Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta
22ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
23Zan aika da annoba a kanta
24“ ‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
25“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub.
26Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”