We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Mai Hadishi 3

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Mai Hadishi 2 Mai Hadishi Mai Hadishi 4 →

1Akwai lokaci domin kowane abu,

2Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,

3Lokacin kisa da lokacin warkarwa,

4Lokacin kuka da lokacin dariya,

5Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su,

6Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya,

7Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa,

8Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya,

9Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa?

10Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane.

11Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.

12Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai.

13Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.

14Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi.

15Duk abin da yana nan ya taɓa kasancewa,

16Sai na ga wani abu kuma a duniya,

17Sai na yi tunani a zuciyata,

18Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba.

19Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani.

20Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma.

21Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”

22Saboda haka na ga babu abin da ya fi kyau wa mutum fiye da yă more wahalar aikinsa, domin wannan ne rabonsa. Gama wa zai kawo shi yă ga abin da zai faru a bayansa?

← Mai Hadishi 2 Mai Hadishi Mai Hadishi 4 →