1Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa,
2gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma.
3Suka sāke tā da murya suka ce,
4Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce,
5Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa,
6Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,
7Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna
8Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta
9Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”
10Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”
11Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.
12Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi.
13Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne.
14Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin.
15Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki.
16A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce,
17Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah,
18don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.”
19Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa.
20Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci.
21Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.