1Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa.
2Ya yi kira da babbar murya ya ce,
3Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin
4Sai na ji wata murya daga sama ta ce,
5gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama.
6Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku;
7Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki
8Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata,
9“Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita.
10Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa,
11“Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu
12kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi;
13kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.
14“Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’
15Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki
16su ce,
17Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’
18Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’
19Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa,
20“Ki yi murna a kanta, ya sama!
21Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce,
22Ba za a ƙara jin
23Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa
24A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka,