1Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona,
2Ku je Kalne ku dube ta;
3Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana
4Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa
5Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi
6Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi
7Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta;
8Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta,
9Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu.
10In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”
11Gama Ubangiji ya ba da umarni,
12Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu?
13ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar6.13 Lo Debar yana nufin wofi. da yaƙi
14Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce,