We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

1 Tarihi 8

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← 1 Tarihi 7 1 Tarihi 1 Tarihi 9 →

1Benyamin shi ne mahaifin,

2Noha na huɗu da Rafa na biyar.

3’Ya’yan Bela maza su ne,

4Abishuwa, Na’aman, Ahowa,

5Gera, Shefufan da Huram.

6Waɗannan su ne zuriyar Ehud, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Geba waɗanda aka kuma kwasa zuwa Manahat.

7Na’aman, da Ahiya, da Gera. Gera ne shugabansu lokacin da aka kai su bauta, shi ne ya haifi Uzza da Ahilud.

8An haifa ’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara.

9Ya haifi Yobab, Zibiya, Hodesh, Malkam,

10Yewuz, Sakiya da Mirma ta wurin Hodesh matarsa. Waɗannan su ne ’ya’yansa, kawunan iyalai.

11Ya haifi Abitub da Efa’al ta wurin Hushim.

12’Ya’yan Efa’al maza su ne,

13da Beriya da Shema, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Aiyalon waɗanda kuma suka kori mazaunan Gat.

14Ahiyo, Shashak, Yeremot

15Zebadiya, Arad, Eder,

16Mika’ilu, Isfa da Yoha su ne ’ya’yan Beriya maza.

17Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber,

18Ishmerai, Izliya da Yobab su ne ’ya’yan Efa’al maza.

19Yakim, Zikri, Zabdi,

20Eliyenai, Zilletai, Eliyel,

21Adahiya, Berahiya da Shimra su ne ’ya’yan Shimeyi maza.

22Ishfan, Eber, Eliyel,

23Abdon, Zikri, Hanan,

24Hananiya, Elam, Antotiya,

25Ifdehiya da Fenuwel su ne ’ya’yan Shashak maza.

26Shamsherai, Shehariya, Ataliya,

27Ya’areshiya, Iliya da Zikri su ne ’ya’yan Yeroham maza.

28Dukan waɗannan su ne kawunan iyalai, manya kamar yadda aka lissafta a cikin zuriyarsu, suka zauna a Urushalima.

29Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon.

30ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,

31Gedor, Ahiyo, Zeker

32da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.

33Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.

34Ɗan Yonatan shi ne,

35’Ya’yan Mika maza su ne,

36Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.

37Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel.

38Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu.

39’Ya’yan ɗan’uwansa Eshek su ne,

40’Ya’yan Ulam maza jarumawa ne sosai waɗanda suke iya riƙe baka. Suna da ’ya’ya maza masu yawa da jikoki, 150 gaba ɗaya.

← 1 Tarihi 7 1 Tarihi 1 Tarihi 9 →