We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Zakariya 13

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Zakariya 12 Zakariya Zakariya 14 →

1“A ranan nan za a buɗe maɓulɓulan ruwa zuwa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima, don a tsarkake su daga zunubi da rashin tsabta.

2“A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar.

3In kuma wani ya yi annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’ad da yake yin annabci, iyayensa za su soke shi da takobi.

4“A ranan nan kowane annabi zai ji kunyar annabcin wahayinsa. Ba zai sa rigar annabci mai gashi ba don yă yi ruɗu.

5Zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne. Ni manomi ne; ƙasa ce nake samun abin zaman gari tun ina matashi.’13.5 Ko kuwa manomi; wani mutum ya sayar da a ƙuruciyata

6In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka13.6 Ko kuwa miyaku a tsakanin hannuwanka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’

7“Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina,

8A cikin ƙasar duka,” in ji Ubangiji,

9Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta;

← Zakariya 12 Zakariya Zakariya 14 →