1Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?
2Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba,
3Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan;
4A gare ka ne kakanninmu suka sa bege;
5Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto;
6Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba,
7Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a;
8“Ya dogara ga Ubangiji;
9Duk da haka ka fitar da ni daga ciki;
10Daga haihuwa an jefa ni a kanka;
11Kada ka yi nesa da ni,
12Bijimai masu yawa sun kewaye ni;
13Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama
14An zubar da ni kamar ruwa,
15Ƙarfina ya bushe kamar kasko,
16Karnuka sun kewaye ni;
17Zan iya ƙirga ƙasusuwana;
18Sun raba rigunana a tsakaninsu
19Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa;
20Ka ceci raina daga takobi,
21Ka cece ni daga bakin zakoki;
22Zan furta sunanka ga ’yan’uwana;
23Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi!
24Gama bai rena ko yă ƙyale
25Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro;
26Matalauta za su ci su ƙoshi;
27Dukan iyakokin duniya
28gama mulki na Ubangiji ne
29Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada;
30Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima;
31Za su yi shelar adalcinsa