1Bayan annobar, sai Ubangiji ya yi magana da Musa da Eleyazar ɗan Haruna, firist ya ce,
2“Ku ƙidaya dukan jama’ar Isra’ila daga mai shekaru ashirin zuwa gaba da za su iya aikin sojan Isra’ila.”
3Musa da Eleyazar firist suka yi musu magana a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko, suka ce,
4“Ku ƙidaya maza daga mai shekara ashirin zuwa gaba yadda Ubangiji ya umarci Musa.”
5Zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila,
6daga Hezron, kabilar Hezronawa;
7Waɗannan su ne kabilan Ruben; jimillarsu ta kai 43,730.
8Ɗan Fallu kuwa shi ne Eliyab,
9’ya’yan Eliyab maza kuwa su ne, Nemuwel, Datan da Abiram. Datan da Abiram nan, su ne shugabannin mutanen da suka tayar wa Musa da Haruna, suna kuma cikin waɗanda suka bi Kora sa’ad da ya tayar wa Ubangiji.
10Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora, wanda ƙungiyarsa ta mutu sa’ad da wuta ta cinye mutum 250. Wannan kuwa ya zama alamar faɗakarwa.
11Amma fa, zuriyar Kora ba tă mutu ba.
12Zuriyar Simeyon bisa ga kabilansu,
13daga Zera, kabilar Zerawa;
14Waɗannan su ne kabilan Simeyon; jimillarsu ta kai 22,200.
15Zuriyar Gad bisa ga kabilansu,
16daga Ozni, kabilar Ozniyawa
17daga Arod, kabilar Arodiyawa;
18Waɗannan su ne kabilan Gad, jimillarsu ta kai 40,500.
19Er da Onan, ’ya’yan Yahuda ne, amma sun mutu a Kan’ana.
20Zuriyar Yahuda bisa ga kabilansu,
21Zuriyar Ferez kuwa,
22Waɗannan su ne kabilan Yahuda; jimillarsu ta kai 76,500.
23Zuriyar Issakar bisa ga kabilansu,
24daga Yashub, kabilar Yashubawa;
25Waɗannan su ne kabilan Issakar; jimillarsu ta kai 64,300.
26Zuriyar Zebulun bisa ga kabilansu,
27Waɗannan su ne kabilan Zebulun, jimillarsu ta kai 60,500.
28Zuriyar Yusuf bisa ga kabilansu ta wurin Manasse da Efraim.
29Zuriyar Manasse,
30Waɗannan su ne zuriya Gileyad,
31daga Asriyel, kabilar Asriyelawa;
32daga Shemida, kabilar Shemadawa;
33(Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.)
34Waɗannan su ne kabilan Manasse, jimillarsu ta kai 52,700.
35Waɗannan su ne kabilan Efraim bisa ga kabilansu,
36Waɗannan su ne kabilan Shutelawa,
37Waɗannan su ne kabilan Efraim; jimillarsu ta kai 32,500.
38Zuriyar Benyamin bisa ga kabilansu,
39daga Shufam, kabilar Shufamawa;
40Zuriyar Bela daga Ard da Na’aman,
41Waɗannan su ne kabilan Benyamin, jimillarsu ta kai 45,600.
42Waɗannan su ne kabilan Dan bisa ga kabilarsu,
43Dukansu kabilan Shuhamawa ne, jimillarsu ta kai 64,400.
44Zuriyar Asher bisa ga kabilansu,
45daga zuriyar Beriya kuwa,
46(Asher yana da ’ya mace da ake kira Sera.)
47Waɗannan su ne kabilan Asher; jimillarsu ta kai 53,400.
48Zuriyar Naftali bisa ga kabilansu,
49daga Yezer, kabilar Yezerawa;
50Waɗannan su ne kabilan Naftali, jimillarsu ta kai 45,400.
51Dukan jimillar mazan Isra’ila ta kai 601,730.
52Ubangiji ya ce wa Musa,
53“Ka rarraba musu ƙasar a matsayin gādo, bisa ga yawan kabila.
54Ga ƙungiya mafi girma, ka ba ta rabo mafi girma; ga ƙaramar ƙungiya kuwa, ka ba ta ƙarami rabo; kowane zai karɓa rabonsa ga yawan mutanen da aka rubuta.
55Ka tabbatar an rarraba ƙasar ta wurin rabo. Abin da kowace ƙungiya ta gāda zai zama bisa ga sunayen kabilar kakanninta.
56Za a raba kowane gādo bisa ga rabo tsakanin manyan da ƙanana ƙungiyoyi.”
57Waɗannan su ne Lawiyawa da a ƙidaya bisa ga kabilansu,
58Waɗannan kuma su ne kabilan Lawiyawa,
59sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa26.59 Ko kuwa Yokebed, ’yar Lawi, wadda aka haifa wa Lawi a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma ’yar’uwarsu Miriyam.
60Haruna shi ne mahaifin Nadab, Abihu, Eleyazar da kuma Itamar.
61Amma Nadab da Abihu sun mutu sa’ad da suka miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.)
62Dukan ’ya’yan Lawiyawa maza daga wata ɗaya zuwa gaba, jimillarsu ta kai 23,000. Ba a ƙidaya su tare da sauran Isra’ilawa ba, domin ba a ba su gādo tare da su ba.
63Waɗannan su ne waɗanda Musa da Eleyazar firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a filaye Mowab kusa da Urdun a hayen Yeriko.
64Ba ko ɗayansu da yake cikin waɗanda Musa da Haruna firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a Hamadar Sinai.
65Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.