We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Ƙidaya 24

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Ƙidaya 23 Ƙidaya Ƙidaya 25 →

1To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada.

2Da Bala’am ya duba sai ya ga Isra’ila sun yi sansani kabila, kabila, Ruhun Allah kuwa ya sauko masa,

3sai ya yi annabcinsa ya ce,

4maganar mutumin da ya saurari maganar Allah,

5“Ina misalin kyan tentunanka, ya Yaƙub,

6“Kamar kwaruruka suke a shimfiɗe,

7Ruwa zai kwararo daga bokitinsu;

8“Allah ya fitar da su daga Masar;

9Kamar zaki sun laɓe sun kwanta,

10Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku.

11Yanzu ka bar nan ka tafi gida! Na ce zan sāka maka da lada mai kyau, amma Ubangiji ya hana ka samun ladan.”

12Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa ’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa,

13‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’?

14Yanzu zan koma wajen mutanena, amma bari in gargaɗe ka game da abin da mutanen nan za su yi wa mutanenka cikin kwanaki masu zuwa.”

15Sa’an nan ya furta saƙonsa.

16maganar mutumin da ya saurari maganar Allah,

17“Na gan shi, amma ba yanzu ba;

18Za a ci Edom da yaƙi;

19Mai mulki zai fito daga Yaƙub

20Sai Bala’am ya ga Amalek, ya kuma furta maganarsa.

21Sai ya ga Keniyawa, ya kuma furta maganarsa.

22duk da haka, za a hallaka ku Keniyawa

23Sai ya furta maganarsa ya ce,

24Jiragen ruwa za su zo daga Kittim;

25Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa.

← Ƙidaya 23 Ƙidaya Ƙidaya 25 →