We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Ibraniyawa 1

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

Ibraniyawa Ibraniyawa 2 →

1A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,

2amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya.

3Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.

4Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.

5Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa,

6Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce,

7Da yake magana game da mala’iku kuwa ya ce,

8Amma game da Ɗan ya ce,

9Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta;

10Ya kuma ce,

11Su za su hallaka, amma kai kana nan;

12Za ka naɗe su kamar mayafi,

13Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa,

14Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?

Ibraniyawa Ibraniyawa 2 →