1Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim.
2Ibrahim ya haifi Ishaku,
3Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu;
4Ram ya haifi Amminadab,
5Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa,
6Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda.
7Solomon ya haifi Rehobowam,
8Asa ya haifi Yehoshafat,
9Azariya ya haifi Yotam,
10Hezekiya ya haifi Manasse,
11Yosiya kuma ya haifi Yekoniya1.11 Wato, Jehohiyachin; haka ma a aya 12 da ’yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.
12Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon.
13Zerubbabel ya haifi Abiyud,
14Azor ya haifi Zadok,
15Eliyud ya haifi Eleyazar,
16Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.
17Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.1.17 Ko kuwa Kiristi. Kiristi (Da Girik) Almasihu (Da Ibraniyanci) duk suna nufin “Shafaffe.”
18Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
19Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye.
20Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.
21Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu,1.21 Yesu da Girik shi ne Yoshuwa da Ibraniyanci, wanda yake nufin Ubangiji yana ceto. gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”
22Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa,
23“Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel”1.23 Ish 7.14 (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).
24Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa.
25Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.