We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Ayuba 39

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Ayuba 38 Ayuba Ayuba 40 →

1“Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa?

2Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu?

3Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu;

4’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji;

5“Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi?

6Na sa jeji yă zama gidansa

7Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari;

8Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa

9“Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci?

10Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya?

11Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa?

12Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida

13“Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki

14Tana sa ƙwai nata a ƙasa

15ba tă damu ko za a taka su a fasa su,

16Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba

17Gama Allah bai ba ta hikima ba

18Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu

19“Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa

20Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra,

21Yana takawa da ƙarfi

22Yana yi wa tsoro dariya

23Kwari a baka yana lilo a gabansa

24Yana kartar ƙasa da ƙarfi;

25Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’

26“Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya

27Ko da umarninka ne shaho yake firiya

28Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare;

29Daga can yake neman abincinsa;

30’Ya’yansa suna shan jini,

← Ayuba 38 Ayuba Ayuba 40 →