1Sai Ayuba ya amsa,
2“Ku saurare ni da kyau;
3Ku ba ni zarafi in yi magana,
4“A wurin mutum ne na kawo kukana?
5Ku dube ni, ku kuma yi mamaki;
6Lokacin da na yi tunanin wannan,
7Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa,
8Suna ganin ’ya’yansu suna girma,
9Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba.
10Shanunsu ba sa fasa haihuwa;
11Suna aika ’ya’yansu kamar garke;
12Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya;
13Suna yin rayuwarsu cikin arziki
14Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’
15Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa?
16Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba
17“Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa?
18Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska,
19An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’
20Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka;
21Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya
22“Wani zai iya koya wa Allah ilimi
23Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi
24jikinsa ɓulɓul,
25Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai,
26Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa,
27“Na san duk abin da kuke tunani,
28Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan,
29Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba?
30cewa an kāre mugu daga ranar bala’i,
31Wane ne yake gaya masa abin da ya yi?
32Za a bizne shi a kabari,
33Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali;
34“Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya