We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Yoshuwa 12

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Yoshuwa 11 Yoshuwa Yoshuwa 13 →

1Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.

2Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.

3Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.

4Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.

5Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.

6Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.

7Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.

8Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

9Sarkin Yeriko, ɗaya

10sarkin Urushalima, ɗaya

11sarkin Yarmut, ɗaya

12sarkin Eglon, ɗaya

13sarkin Debir, ɗaya

14sarkin Horma, ɗaya

15sarkin Libna, ɗaya

16sarkin Makkeda, ɗaya

17sarkin Taffuwa, ɗaya

18sarkin Afek, ɗaya

19sarkin Madon, ɗaya

20sarkin Shimron Meron, ɗaya

21sarkin Ta’anak, ɗaya

22sarkin Kedesh, ɗaya

23sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya

24sarki Tirza, ɗaya.

← Yoshuwa 11 Yoshuwa Yoshuwa 13 →