We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Irmiya 23

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Irmiya 22 Irmiya Irmiya 24 →

1“Kaiton makiyayan da suka hallakar suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji.

2Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana ce wa makiyayan da suke lura da mutanena, “Domin kun watsar da garkena kuka kuma kore su ba ku kuma lura da su ba, zan kawo hukunci a kanku saboda muguntar da kuka yi,” in ji Ubangiji.

3“Ni kaina zan tattara raguwar garkena daga ƙasashen da na kore su zuwa zan kuma dawo da su ga makiyayansu, inda za su yi ta haihuwa su riɓaɓɓanya.

4Zan sa makiyaya a kansu waɗanda za su lura da su, ba za su ƙara jin tsoro ko razana ba, ba kuwa waninsu da zai ɓace,” in ji Ubangiji.

5“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji,

6A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda

7“Saboda haka fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da mutanen ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da Isra’ila daga Masar ba,’

8amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da zuriyar Isra’ila daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashen da ya yashe su.’ Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu.”

9Game da annabawa kuwa,

10Ƙasar ta cika da mazinata;

11“Annabi da firist dukansu biyu marasa sanin Allah ne;

12“Saboda haka hanyarsu za tă yi santsi;

13“A cikin annabawan Samariya

14A cikin annabawan Urushalima kuma

15Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa,

16Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,

17Suna cin gaba da ce wa waɗanda suka rena ni,

18Amma wane ne a cikinsu ya taɓa tsaya a majalisar Ubangiji

19Ga shi, hadarin Ubangiji

20Fushin Ubangiji ba zai kau ba

21Ban aiki waɗannan annabawa ba,

22Amma da a ce sun tsaya a majalisata,

23“Ni ɗin Allah na kusa ne kawai,”

24Akwai wanda zai iya ɓuya a lungu har da ba zan iya ganinsa ba?”

25“Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’

26Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu?

27Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada.

28Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji.

29“Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse?

30“Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna.

31I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya furta.’

32Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.

33“Sa’ad da waɗannan mutane, ko annabi ko firist, ya tambaye ka, ‘Mece ce maganar23.33 Ko kuwa nawaya (dubi Seftuwajin da Bulget) Ubangiji?’ Ka ce musu, ‘Wace magana?23.33 Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Bulget Ku ne nawayar. (Ibraniyanci na faɗar Ubangiji da nawaya sun yi kama da juna.) Zan yashe ku, in ji Ubangiji.’

34In annabi ko firist ko da wani dabam ya ce, ‘Wannan ne abin da Ubangiji yake cewa,’ zan hukunta wannan mutum da kuma gidansa.

35Ga abin da kowannenku yana cin gaba da ce wa abokinsa ko danginsa, ‘Mece ce amsar Ubangiji?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’

36Amma kada ku ƙara ambatar ‘maganar Ubangiji’ domin kowace maganar mutum kan zama maganarsa. Ta haka kukan lalace maganar Allah mai rai, Ubangiji Maɗaukaki, Allahnmu.

37Ga abin da za ku ci gaba da faɗa wa annabi, ‘Mece ce amsar Ubangiji gare ka?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’

38Ko da yake kuna cewa, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ga abin da Ubangiji yana cewa kuna amfani da kalmomi, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ko da yake na ce muku kada ku ce, ‘Wannan ce maganar Ubangiji.’

39Saboda haka, tabbatacce zan manta da ku in kuma jefar da ku daga gabana tare da birnin da na ba ku da kuma kakanninku.

40Zan kawo muku madawwamiyar kunya, kunya ta har abada wadda ba za a taɓa manta ba.”

← Irmiya 22 Irmiya Irmiya 24 →