1“An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe,
2Har ’ya’yansu ma sun tuna
3Dutsena a ƙasar
4Saboda laifinku za ku rasa
5Ga abin da Ubangiji yana cewa,
6Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;
7“Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,
8Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa
9Zuciya ta fi kome ruɗu
10“Ni Ubangiji nakan bincike zuciya
11Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba
12Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko,
13Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila,
14Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;
15Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take?
16Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba;
17Kada ka zama mini abin razana;
18Bari masu tsananta mini su sha kunya,
19Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima.
20Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi.
21Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima.
22Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku.
23Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba.
24Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba,
25sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada.
26Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji.
27Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ”